Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka ta Nuna Bacin Ranta da Bangarorin Dake Fafatawa a Sudan ta Kudu


John Kerry Sakataren Harkokin Wajen Amurka

Amurka ta caccaki bangarorin shugaban kasar Suda ta Kudu da abokin hamayarsa akan rashin cimma daidato wajen kafa gwamnatin hadin kai na kasa ganin yadda 'yan kasar ke shan azaba da shugabannin suka haddasa kana yara suna mutuwa sabili da muguwar yunwa da ta addabi kasar.

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya caccaki bangarorin kasar Sudan ta kudu da kakkausan lafazi bayan da suka kasa kafa gwamnatin wucin gadi cikin wa'adin da aka bayar. Kerry ya fada cewa gazawar shugabannin ba komi ba ne illa cin mutuncin 'yan kasar ne da kuma jefasu cikin mawuyacin hali na ba gaira ba dalili.

A wata sanarwar da ya gabatar shekaranjiya Litinin John Kerry yace duk bangarorin kasar, wato, gwamnantin kasar da yan tawayen babu wanda ya ke da nufin kawo shawarwarin da zasu kai ga samun zaman lafiya tsakani da Allah.

Yace cikin watani shidda da suka yi suna yin shawarwari a kasar Habasha an sha wuce wa'adin da aka tsayar ba tare da tsinana komai ba, a yayinda mutane da basu san hawa ba balle sauka suke ta mutuwa wasu kuma da dama suna cikin muguwar yunwa inda yanzu ma yara sai mutuwa suke yi.

Yarjejeniyar da aka kula a watan Mayu ta tanadi cewa shugaba Salva Kir da abokin hamaiyarsa Riek Machar suyi alkawarin kafa gwamnatin hadin kan kasa a ranar goma ga watan Augusta.

Fafatawa tsakanin sojojin dake biyaya ga shugabanin biyu ya kashe akallla mutane dubu goma tun watan Disamba.

A saboda haka John Kerry ya bukaci kungiyar kasashen Afrika da kungiyar kasashen Afrika ta gabas da ake kira IGAD a takaice da su dauki wani mataki nan take. Kerry ya lura cewa a baya wadannan kungiyoyi sun bukaci a dauki mataki mai tsanani idan bangarorin suka kasa kafa gwamnati cikin wada'in da aka basu.

Kawo yanzu dai ba'a samu wata daidaituwa ba tsakanin shugaban kasar da abokin hamayarsa.

XS
SM
MD
LG