Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Saka Takunkumi Kan Kamfanin Man Venezuela


Wasu manyan jami'an gwamnatin Amurka

Amurka ta kakabawa kamfanin man kasar Venezuela takunkumi, tana mai cewa, matakin kokari ne na adana dukiyar al’ummar Venezuela.A jiya Litinin, mai bayar da shawara ga kasa kan tsaro John Bolton, ya ce danniya da tsananin fatara da Shugaba Nicolas Maduro da gwamnatinsa suka haddasa, sun ishi mutanen Venezuela.

“Matakin da aka dauka yau zai tabbatar da cewa daga yanzu ba za su iya wawushe dukiyar mutanen Venezuela ba,” inji Bolton.

Takunkumin ya tanadi kwace kaddarorin kamfanin man na PDVSA mallakin gwamnatin Venezuela a duk inda suke a Amurka.

Hakazalika, an haramta ma kamfanoni da kuma ‘yan kasuwar Amurka yin hulda da kamfanin.

Reshen kamfanin a Amurka mai suna “Citgo” wanda ke tace man kasar Venezuela, da kuma sayar da man kasar ta Venezuela a Amurka, zai ci gaba da gudanar da harkokinsa kamar yadda ya saba.

Sai dai duk wani kudin shiga da kamfanin na Citgo ya samu za a sa ne a wani asusu.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG