Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Sakawa Sudan ta Kudu Takunkumi


Sakatare Kerry.

​Amurka ta ba da sanarwar kakaba takunkuminta na farko kan Sudan Ta Kudu, inda fafatawar da ake yi tsakanin dakarun da ke goyon bayan gwamnati da masu adawa da ita ta yi sanadin mutuwar dubban mutane tun daga tsakiyar watan Disamba.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry ya ce Amurka za ta kakaba takunkumin kudi kan Marial Chanuong, wani kwamandan sojojin gwamnati da Peter Gadet, wani jagoran sojoji mai biyayya ga tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Riek Machar.

A yayin wata ganawarsu da Shugabar Sashen Hulda da Kasashen da ba su Tarayyar Turai, Catherin Ashton, Kerry ya ce mutanen biyu sun taka rawa wajen yada munanan tashe-tashen hankula kan fararen hula.

Takunkumin ya tanaji kame duk wata kadara da mutane biyun ke da ita a Amurka. Wannan hukuncin ya kuma haramta ma Amurkawa da duk wani kamfanin Amurka yin wata huldar kasuwanci da mutanen.
XS
SM
MD
LG