Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Sake Jaddada Goyon Bayanta Ga Masu Zanga-zanga A Iran


Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Nikki Haley

A wani mataki na karfafa gwiwar masu zanga-zangar bijirewa manufofin gwamnati a Iran, Amurka ta ce za ta taimaka ma masu zanga-zangar ta kuma ladabtar da wadanda su ka danne masu zanga-zangar karfi da yaji.

Amurka ta yi alkawarin taimaka ma masu zanga-zanga a Iran, ta na mai yin tir da jami’an gwamnatin Iran, saboda irin matakin da su ka dauka na murkushe zanga-zangar, matakin da ya yi sanadin mutuwar mutane 21 da kuma kama mutane sama da 1,000.

Wani jami’in Fadar Shugaban Amurka ta White House, jiya Alhamis ya ce Amurka za ta zakulo irin bayanan da ke bukatar daukar mataki, za kuma ta dubi yiwuwar kara kakaba ma Iran sabbin takunkumi ga wadanda su ka danne zanga-zangar da aka fara a makon jiya kawai.

Sannan a MDD kuma, Jakadiyar Amurka Nikki Haley ta bukaci a yi wani zama na gaggawa yau Jumma’a game da wannan al’amarin.

To amma kasar Rasha da wasu mambobin Kwamitin Sulhun MDD na sukar wannan kiran taron da Amurka ta yi, su na cewa wannan zanga-zangar al’amari ne na cikin gida.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG