Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Sanar Da MDD Shirinta Na Ficewa Daga WHO


Shugaban Amurka Donald Trump (Hagu) da Shugaban WHO, Tedros Adhanom Ghebereysus (dama)
Shugaban Amurka Donald Trump (Hagu) da Shugaban WHO, Tedros Adhanom Ghebereysus (dama)

Bayan watanni da ya kwashe yana nuna rashin gamsuwarsa kan abin da ya kira "'yar amshin shatar China" da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta zama, Shugaban Amurka Donald Trump ya mika takardar sanar da ficewar kasar daga hukumar ta WHO.

Fadar White House ta sanar da Majalisar Dinkin Duniya a hukumance cewa, Amurka za ta janye daga Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, duk da cewa adadin masu kamuwa da cutar COVID-19 sai karuwa yake yi a kasar.

Shugaba Donald Trump ya dakatar da tallafin da Amurka ke baiwa Hukumar ta WHO a watan Afrilu sannan bayan wata daya ya sanar da aniyyarsa ta ficewa daga hukumar.

Trump ya zargi WHO da zama ‘yar amashin shatar China dangane da yadda ta tafiyar da yaki da cutar coronavirus, ya kuma nemi ta yi sauye-sauye kan yadda take gudanar da al’amuranta- sharadin da Trump ya ce WHO din ta gaza cikawa.

A karkashin dokokin WHO, kowace kasa da za ta bar hukumar, dole ne ta ba da sanarwa shirin ficewa na tsawon shekara guda.

Sai dai kuma idan Trump ya fadi zabe mai zuwa a watan Nuwamba, shugaban Amurka na gaba zai iya yanke hukuncin ci gaba da zama a hukumar

Ita dai Amurka, ta fi kowacce kasa yawan mutanen da ke dauke da cutar COVID-19 inda take da adadin mutum miliyan 3 – sannan kusan mutum 131,000 suka mutu sanadiyyar cutar.

Masana a fannin kiwon lafiya sun soki wannan mataki da shugaban ya dauka inda suka ce “babu hangen nesa a cikinsa” kuma zai ruguza dadaddiyar dangantakar da ke tsakanin bangarorin biyu wacce aka kwashe gomman shekaru ana yaki da cututtuka.

Amurka cikakkiyar mamba ce a Hukumar ta WHO, wacce aka kafa a shekarar 1948, kuma ita ce kasar da ta fi baiwa hukumar tallafi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG