Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Shirya Ta Kashe Har Dala Miliyan 60 Domin Yaki da Ta'addanci a Yankin Sahel


Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Nikki Haley
Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Nikki Haley

A wajen taron kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya jakadiyar Amurka Nikki Haley ta sanar da taimakon kudi dalar Amurka miliyan sittin domin yaki da ta'addanci a kasashen yankin sahel da suka hada da Burkina Faso, Chadi,Mali, Mauritania, da Nijar

Amurka ta yi alkawarin kashe kudade har zuwa Dala Miliyan 60 domin taimakawa yaki da ta’addanci a kasashen yankin sahel a nahiyar Afirka.

Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson, wanda shine ya sanar da taimakon, yace Amurka zata taimakawa rundunar sojan nan ta kasashen yankin sahel su biyar da aka hada a farkon shekarar nan, wanda suka hada da hadakar sojojin Burkina Faso da Chadi da Mali da Mauritania da kuma Nijar.

A taron kwamitin tsaro na MDD akan kungiyar hadin gwiwar kasashen yankin sahel jiya Litinin, jakadiyar Amurka Nikki Haley, ta bayyana cewa tallafin da za a bayar zai ta’allaka ne akan dangatakar diflomasiya kuma dole ne sai ‘yan Majalisar Dokokin Amurkasun amince kafin a bayar da shi, sannan kuma ba za a bayar da shi ba ta hannun MDD.

Cikin makonni masu zuwa, kwamitin tsaron MDD zai tattauna zabi hudu da ake da su, da MDD zata yi amfani don tabattarda an yi anfani da kuddi don tabbatar da ganin rundunar sojan ta tafiyar da aikinta yadda aka tsara shi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG