Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Taimakawa Zirin Gaza Da Dola Miliyan 212


Sakataren harakokin wajen Amurka John Kerry ya na magana da ministan harakokin wajen Jordan Nasser Judeh a taron Babban Alkahira

Kasashe da dama sun yi babban taro a kasar Masar a kan sake gina Zirin Gaza

Gwamnatin kasar Amurka ta yiwa Falasdinawa alkawarin sabon taimakon dola miliyan 212, ta yi alkawarin ne a wajen wani babban taron tara kudin sake gina Zirin Gaza da yaki ya afkawa.

Sakataren harakokin wajen Amurka John Kerry ne yayi sanarwar taimakawa da kudaden a birnin Alkahira a yau Lahadi , ya na mai cewa a halin yanzu al'ummar Gaza ke matukar bukatar taimako. Da ma dai gwamnatin Amurka ta riga ta bada dola miliyan 118 na ayyukan agajin jin kai.

Dola biliyan hudu, wato dola miliyan dubu hudu shugabannin Falasdinawa ke bukata daga dimbin kasashen dake halartar babban taron.

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya kara jaddada irin bannar da aka yi mu su sannan kuma ya kara jaddada bukatar taimakon, ya ce unguwanni baki daya aka rugurguza a cikin yakin da Israila ta yi kwanaki 50 ta na yi da Hamas. Yakin ya kashe Falasdinawa fiye da 2,100, akasarin su fararen hula a yayin da ita Israila ta yi asarar sojojin ta 67 da fararen hula 6.

Shugaban kasar Masar Abdel Fattah el-Sissi ya bukaci Israila ta kaddamar da sabbin tattaunawar sulhun da za su dogara bisa wata shawarar shekarar 2002 wadda ta kunshi cewa Israila ta fice daga yankunan da ta kama lokacin yakin GTT a shekarar 1967.

shugaban kasar Masar Abdel Fattah el-Sissi
shugaban kasar Masar Abdel Fattah el-Sissi

Shi ma Sakatare Kerry yayi kira ga dukan su, su kudiri sabuwar aniyar yin aikin samar da zaman lafiyar da dukan su za su gamsu.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG