Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Tsawaita Wa'adin Kariyar Da Take Bai wa 'Yan Liberia


Wasu 'yan kasar Liberia
Wasu 'yan kasar Liberia

Gwamnatin shugaba Donald Trump za ta kawo karshen wani shiri da ke bai wa ‘yan asalin Liberia da ke zaune a Amurka damar kaucewa fitar da su ta anyar tursasawa daga Amurka.

Shirin da ake mai da mutane kasashen su tilas da ake kira DED a takaice, an kara masa shekara daya, a maimakon a dakatara da shi a ranar Asabar mai zuwa.

A yanzu Liberia ta dai na fuskantar rikici kuma ta samu gagarumin ci gaba kan maido da zaman lafiya da gwamnatin dimokradiyya, a cewar wata sanarwar da shugaba Trump ya rattabawa hanu da fadarsa ta White House ta fitar.

A karkashin wani shirin da aka fara a shekara 1991 mai suna T-P-S ne aka tanadarwa wasu ‘yan kasar Liberia daman zama a Amurka don gujewa rikici da yakin basasar da kasarsu ke fuskanta a lokacin.

Yanzu dai shi wannan shirin hana maida ‘yan Liberia kasarsu zai kare ne ranar 31 ga watan Maris din shekara mai zuwa ta 2019.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG