Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Yi Alla-wadai Da China - Pompeo


Sakataren Harkokin Tsaron Amurka, Mike Pompeo
Sakataren Harkokin Tsaron Amurka, Mike Pompeo

Amurka na zargin kasar China da yin amfani da halin da ake ciki na annobar COVID-19, wajen ‘kara kaimin ayyukan sojinta a kusa da Taiwan da kuma tekun kudancin China.

“Amurka, da kakkausar murya, ta yi Alla-wadai da zaluncin China,” a cewar Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo, gabannin taron da aka yi tsakanin Amurka da ministocin kungiyar kasashen kudu maso gabashin yankin Asiya.

Pompeo ya kara da cewa “haka kuma muna ganin yadda China ke amfani da karfin soji wajen matsawa Taiwan lamba, da sauran makwabtanta da ke tekun kudancin China, har ma ta kai ga nutsar da wani jirgin kamun kifi na kasar Vietnam."

"Muna fatan sauran kasashe zasu tuhume su da laifin da suka aikata,” abin da ya fadi kenan ‘yan sa’o’i kafin a fara taron ministocin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG