Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Yi Allah Wadai Da Harin Da Aka Kai Garin Mubi


Amurka ta yi Allah wadai da harin kunar bakin wake da aka kai garin Mubi, dake jihar Adamawa.

A wata sanarwa da fadar shugaban Amurka ta White House ta fitar da yammacin ranar Alhamis, ta ce da babbar murya Amurka tayi Allah wadai da harin ta’addancin da aka kai masallaci a garin Mubi.

Sanarwar ta ‘kara da cewa irin wadannan hare-haren ta’addanci da ake auna guraren ibada, ya nuna ‘karara irin rashin imanin masu aikata kisan kiyashi ga wadanda basu ji ba basu gani ba.

Kamar yadda shugaban Amurka Donald Trump ya jaddadawa shugaba Buhari, lokacin da ya kai masa ziyarar aiki ranar Litinin da ta gabata, Amurka na tare da Najeriya a yakin da ta ke yi da ta’addanci.

Ranar Talata ne wasu ‘yan kunar bakin wake suka kai hari garin Mubi dake jihar Adamawa, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da jikata wasu dayawa.

Hukumar agajin gaggawa ta Najeriya NEMA ta ce adadin wadanda suka mutu a wannan tagwayen harin kunar bakin wanken sun kai mutane 30, baya ga wadanda aka garzaya da su zuwa cibiyar kiwon lafiya ta gwamnatin tarayya, wato FMC Yola.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG