Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Yi Maraba Da Sakin Fursunonin Siyasa a Sudan


Shugaba Omar al-Bashir na Sudan
Shugaba Omar al-Bashir na Sudan

A wani al'amari na ba sabanba, Amurka ta yi lale marhabin da wani abin da Sudan ta aikata karkashin shugabancin Omar al-Bashir. Sakin fursunonin siyasa da Shugaba al-Bashir ya bayar da umurnin a yi ya burge Amurka.

Jiya Alhamis Amurka ta yi maraba da sakin wasu fursunonin siyasa da aka yi a Sudan, bisa umurnin da Shugaban Sudan Omar al-Bashir ya bayar a farkon wannan satin.

“An saki wasu fursunonin siyasa 54 daga dauri da yammacin ranar 10 ga watan Afirilu bisa da umrurnin da Shugaba Bashir ya bayar, a cewar wata takardar sanarwar da hadakar iyalan wadanda aka sake din ta rubuta,” abin da wani jami’in Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ya gaya ma Muryar Amurka kenan.

Kamfanin dillancin labaran gwamnati (SUNA) ya ce wannan umurni na Shugaba Bashir na daga cikin “matakan sasantawa da hada kan kasa da kuma tabbatar da zaman lafiya” ‘yan makwanni bayan yawan kamen da aka yi da zummar murkushe zanga-zangar kin jinin gwamnati.

A cikin watan Janairu zanga-zanga ta barke a Sudan saboda tsadar burodi da kuma tsare-tsaren tattalin arziki masu tsauri. Zanga-zangar, wadda jam’iyyar ‘yan gurguzu ta taka rawa wajen ruruta ta, ta janyo kama fursunonin siyasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG