Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Tana Tunanin Ko Ta Dauki Matakin Soja Kan Venezuela


Shugaba Trump tareda sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson, da kuma jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley.
Shugaba Trump tareda sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson, da kuma jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley.

Shugaba Trump ne bayyanawa manema labarai haka a gidansa dake jahar New Jersey ranar jumma'a.

Ahalinda ake ciki kuma, shugaban na Amurka Donald Trump, yace matakin soja yana daga cikin zabi da Amurka take dubawa kan kasar Venezuela, ya bayyana hali da ake ciki a kasar a zaman "mai hadari sosai."

Trump wand a ya bayyana haka yayinda yake magana da manema labarai a gidansa dake New Jersey, ya kara da cewa "hakika wannan wani mataki ne da zamu iya dauka." Yace mutanen Venezuela suna cikin wahala suna mutuwa."

Amma a daren jiya Jumma'an, ministan tsaron Venezuela Vladimir Padrino, ya gayawa tashar talabijin ta kasar cewa kalamana na shugaban Amurka "matakai ne na hauka".

Shugaba Trump yace, rikicin da ake yi a Venezuela yana daga cikin ajenda r tattaunawar da yayi da jiya jumma'a, d a sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson, da kuma jakadiyar Amurka a MDD Nikki Haley.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG