Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Za Ta Bude Sabon Ofishin Jakadancinta Na Birnin Qudus


Firai Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu a ranar 28 ga watan Fabrairu

Falasdinawa na adawa da wannan mataki na Amurka, domin a cewarsu, dauke ofishin jakadancin daga Tel Aviv zuwa Birnin Qudus, na nuni da cewa Qudus ya zama babban birnin Isra’ila.

A yau Litinin Amurka za ta bude sabon ofishin jakadancinta da ke Birnin Qudus, inda ta ce za ta hade daukacin ayyukan diplomasiyyanta a sabon ofishin jakadancin.

Wata sanarwa da ma’aikatar harkokokin wajen Amurka ta fitar a jiya Lahadi , ta ce, matakin ba ya nufin Amurka za ta sauya manufofinta ba ne a Birnin Qudus, ko yankin Yammacin Gabar Kogin Jordan ko na Zirin Gaza.

Sanarwar ta kara da cewa, matakin, kokari ne na inganta ayyunkan diplomasiyan Amurka da aikace-aikacenta a yankin.

Falasdinawa na adawa da wannan mataki na Amurka, domin a cewarsu, dauke ofishin jakadancin daga Tel Aviv zuwa Birnin Qudus, na nuni da cewa Qudus ya zama babban birnin Isra’ila.

A watan Oktoban bara, Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo, ya bayyana cewa Amurka za ta mayar da ofishin jakadancinta zuwa Qudus.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG