Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Za Ta Sayarwa Da Sa'udiya Kayan Yaki Na Dala Biliyan Daya


Yarima Muhammad Salman na Saudiya
Yarima Muhammad Salman na Saudiya

Yayinda yake rangadin Amurka yarima mai jiran gado na Saudiya ya samu nasarar sayen makamai daga Amurka da kudinsu ya kai dala miliyan dubu

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta amince da sayarwa kasar Saudi Arabia makamai na dala biliyon daya, yayin da yarima mai jiran-gado na masararutar Saudiyyar yake ci gaba da rangadi a nan Amurka.


An sanar da majalisun Amurka kan yarjejeniyar sayar da makaman a jiya Alhamis, ciki har da makamai masu tarwatsa tankokin-yaki 6,600 da kudinsu ya kai dala miliyon 670 da wasu kayan gyaran motoci da kudinsu ya kai dala miliyon 300 ga sojojin kasar Saudia.


Kasar Saudia itace babbar mai sayen makaman da Amurka ta kera, kuma Amurka tana daukar kasar a matsayin kawarta dake yaki da kungiyoyin al-Qaida da IS a Iraq da Syria.


Masu sukar Saudi Arbia, sun bayyana damuwa a kan sayar mata makaman yayinda take ci gaba da sanya hannu a yakin basasa na tsawon shekaru a Yamal da yan tawayen Houti masu samun goyon bayan Iran.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG