Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Za Ta Tallafawa Pakistan Wajen Farfadowar Mummunar Ambaliyar Da Ta Fuskanta


Cars are seen submerged in flood waters in Morro Bay, California, Jan. 9, 2023 in this picture obtained from social media.
Cars are seen submerged in flood waters in Morro Bay, California, Jan. 9, 2023 in this picture obtained from social media.

A shekarar da ta gabata, kasar Pakistan ta fuskanci ruwan sama kamar da bakin kwarya da mahaukaciyar guguwa mafi karfi da aka gani a tarihin kasar, lamarin da ya haifar da mummunar ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa.

Kimanin mutane miliyan 33 ne ambaliyar ruwan ta shafa, kuma wasu 1,730 suka mutu.

Ƙididdigar da aka gudanar bayan aukuwar bala'in ta ƙiyasta cewa farfado da kasar za ta buƙaci sama da dala biliyan 16.

Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje miliyan biyu, da kuma dubban makarantu, asibitoci da sauran gine-ginen jama'a.

Amurka ta yi alkawarin ba da karin dala miliyan 100 don tallafawa wajen kokarin farfado da Pakistan.

Wannan tallafin kari ne kan dala miliyan 97 na agajin ambaliyar ruwa, jure wa bala'i, da abinci da aka bayar a shekarar 2022.

"Amurka na tare da jama'ar Pakistan kuma ta kuduri aniyar ci gaba da taimaka wa kasar wajen murmurewa daga mummunar ambaliyar."

“Sabon tallafin zai taimaka wajen ƙarfafa yanayin dabarar noma na zamani da samar da abinci; inganta muhimman ayyukan kiwon lafiya a wuraren da ambaliyar ta shafa."

"Hakazalika, tallafin zai taimaka wa abokan huldar Pakistan su sanya hannun jari wajen kariyar jama'a da taimaka wa 'yan kasa, sa ido kan cututtuka, habbakar tattalin arziki, samar da makamashi mai tsafta, da sake gina ababen more rayuwa da suka lalace."

"Muna fatan ci gaba da gina haɗin gwiwar Green Alliance tsakanin Amurka da Pakistan don taimakawa wajen warware ƙalubalen yanayi, tattalin arziki, makamashi, noma, a nan gaba."

XS
SM
MD
LG