Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Za Ta Tsugunar Da 'Yan gudun Hijira Mafi Karanci a Tarihinta


Wasu masu fafutuka suna nuna goyon bayansu ga shigowar 'yan gudun hijira cikin Amurka. Satumba, 14 2017
Wasu masu fafutuka suna nuna goyon bayansu ga shigowar 'yan gudun hijira cikin Amurka. Satumba, 14 2017

A baya, Shugaba Donald Trump ya iyakanta adadin ‘yan gudun hijirar da kasar za ta iya tsugunarwa zuwa 30,000.

Yayin da aka shiga tsakiyar kasafin kudin wannan shekara, Amurka ta kama hanyar tsugunar da ‘yan gudun hijira kalilan, wadanda adadinsu ne mafi karanci a tarihin tsugunar da ‘yan gudun hijira da Amurka ta yi.

Daga ranar 1 ga watan Oktoban 2018 zuwa ranar 31 ga watan Maris na wannan shekarar, ‘yan gudun hijira 151 ne su ka shigo Amurka, aksari daga kasashe uku, wato Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo mai kashi 48% da Burma ma kashi 17% da Ukraine mai kashi 13%, bisa ga alkaluman Ma’aikatar Harkokin Waje.

A baya, Shugaba Donald Trump ya iyakanta adadin ‘yan gudun hijirar da kasar za ta iya tsugunarwa zuwa 30,000.

Wannan ne kuma adadi mafi karanci a tsawon shekaru 40, tun bayan da Majalisar Dokokin Tarayyar kasar ta amince da dokar kula da ‘yan gudun hijra ta 1980.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG