Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Za Ta Wargaza Farfagandar Rasha


John F. Lansing, Shugaban kamfanin BBG, mai kula da Muryar Amurka da sauran kafofin labaran gwamnatin Amurka
John F. Lansing, Shugaban kamfanin BBG, mai kula da Muryar Amurka da sauran kafofin labaran gwamnatin Amurka

Ganin yadda Rasha ke ta yada farfaganda a sassan duniya, Muryar Amurka ta lashi takobin wofinta farfagandar

Amurka za ta yi amfani da wani sabon salo a kafar labarai, wajen mai da martani kan farfagandar da Rasha ke bazawa, inda Amurka za ta yi amfani da labaran gaskiya da zummar dakile labaran karya da Rasha ke yadawa, a cewar babban Shugaban Hukumar Yada Labaran Gwamnatin Amurka, John Lansing ga wani kwamitin Majalisar Dattawa.

Lansing ya fadi jiya Alhamis cewa ya ga abin da ya kira, "karuwar farfaganda da karerayi a duniya," sannan ya ce a yanzu haka cibiyar gwamnati wadda ya ke jagoranta, ta dukufa wajen dakile irin wadannan karerayin ta wajen amfani da gaskiya. BBG ce hukumar da ke kula da Muryar Amurka da sauran kafofin yada labaran gwamnatin Amurka.

Lansing ya bayyana cikakken matakin da hukumar ta BBG ke daukawa, da zummar dakile karyar da Rasha ke yadawa ta wajen tarar abubuwan da Rashawan ke fadi a sassan duniya.

Kwamitocin bincike dabam-dabam na bin diddigin yinkurin Rasha na yin katsalandan a zaben Shugaban kasar Amurka na 2016 da kuma zabukan da aka yi a Turai.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG