Shugaban Amurka Barack Obama yana shirin kyale sojojin Amurka dubu 8,400 a Afghanistan har zuwa karshen wa'adin mulkinsa, matakin da ya bar ayoyin tambaya kan mafita daga rikicin na Afghanistan, yayinda harkokin tsaro suke kara tabarbarewa a kasar, kamar yadda kwararru suka yi la'akari.
Tun farko gwamnatin Obama ta shirya zata rage karfin sojojin Amurka a kasar daga dubu 9,800 dake can ahain yanzu zuwa, dubu 5,500 a karshen wannan shekarar.
Amma shugaban na Amurka jiya Laraba ya bada sanarwar cewa, halin da ake ciki a Afghanistan "bashi da tabbas" saboda haka zai kyale sojoji fiyeda abunda aka tsara tun farko har zuwa 20 ga watan Janairu na badi lokacinda zai sauka daga kan karagar mulki.