Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka zata fara yakar cutar Zika domin dakile yaduwarta


Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama

Wasu manya a fadar shugaban Amurka ta White House sun bayyana cewa, gwamnatin Barack Obama zata karkata akalar kusan Dalar Amurka Miliyan 600 da yawanci a da na yaki da cutar Ebola ne, da cewa za a shiga yakar yaduwar cutar ZIKA da su, duk da yake dai wannan kudade ba za su isa wannan aiki ba.

Za a fara da kudin ne kafin Majalisar Amurka ta dauki mataki akan bukatar gwamantin ta gaggawa da aka mika mata. Kamar yadda shugaban ofishin tsari da kasafin kudi Shaun Donovan ya bayyana. Fadar shugaban kasar dai ya mika bukatar Dala Biliyan 1 da Miliyan 900 ga Majalisar a watan Fabrairun bana.

Fadar White House dai ta yi gargadin cewa, matukar ba a saki kudin wannan aiki ba, to kuwa Amurka na iya fuskantar barazanar kasa shawo kan wannan cutar ta ZIKA daga yaduwa. Wanda ya hada da yiwuwar bata lokacin magance yaduwar sauron, gwaji da kuma rigakafi.

Sakatariyar Ma’aikatar Lafiya da Ayyukan Al’umma Sylvia Burwell tace, a yanzu haka akwai rahotannin da suka shafi cutar ZIKA guda 672 a nan Amurka, da suka hada da wasu mata masu juna biyu guda 64, sai kuma rahoton da aka tabbatar game da cutar a Hawaii.

XS
SM
MD
LG