Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Zata Gana Da China Akan Batun Nukiliyar Koriya


Babban jami’in diflomasiyya na Amurka ya isa China kasa ta uku kuma ta karshe a ziyarar da yake yi a Asiya, inda ya maida hankali akan Shirin Nukiliyar Koriya ta Arewa da ake takaddama a kai.

Sakataren harkokin wajen na Amurka Rex Tillerson ya fada a yau Asabar bayan zaman tattaunawa a Beijing da takwaransa na China, Wang Yi, cewar zaman tankiya a yankin kasashen Koriya ya kai wani mizani mai hatsari.

Babban jami’in diflomasiyyar na Amurka yace “Ina zaton ra’ayin mu guda ne, cewa tankiya tayi tsananin yanzu haka a yankin kasashen”. Ya ci gaba da cewa “Zamu yi aiki tare domin ganin ko zamu iya janyo hankalin Gwamnatin Koriya ta arewa ta sauya alkibla ta kuma kauce daga manufar kera makamian Nukiliya”.

Tillerson ya shirya ganawa da shugaban kasar China Xi Jinping gobe lahadi. Bayan tattaunawa akan Koriya ta Arewa mai yiwuwa su maida hankali akan harkokin kasuwanci da batun takaddamar mallakin wasu yankunan tekun Kudancin China.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG