Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Zata MIka Yakin Afghanistan Ga Sojojin Haya?


Mutuminda ya kafa kamfanin Blackwater Erik Prince.
Mutuminda ya kafa kamfanin Blackwater Erik Prince.

Mai kamfanin sojojin haya anan Amurka Blakwater ne ya bada wannan shawara, wacce take fuskantar turjiya ta ko ina.

Shawarar da mai kamfanin sojojin haya na Amurka da ake kira Blackwater, Mr. Erik Prince, ya bayar cewa Amurka ta mika yakin da take yi a Afghanistan ga sojojin haya, tana fuskantar turjiya a Kabul da kuma anan Washington DC.

Rahotanni suka ce shugaban Amurka Donald Trump, yana nazarin wannan shawara, a tsawon wata daya da ya dauka yana nazarin yakin na Afghanistan, inda yanzu bayan shekaru 16, dakarun Amurka da mayakan sakai na Taliban suke cicirindo.

Shawarar Prince, wanda tsohon sojan ruwa na musamman ne na Amurka ya bayar, tana fuskantar adawa daga tsoffin shugabannin Afghanistan, dama manyan hafsoshin Amurka.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG