Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Za Ta Sayarwa Najeriya Jiragen Yaki Na Zamani


Jiragen yaki na Super Tucano
Jiragen yaki na Super Tucano

Amurka ta amince zata sayarwa da Najeriya Jiragen yaki na zamani samfurin Super Tucano domin ta yaki ta'addanci.

Gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump ta amince sayarwa da Najeriya jiragen saman yakin zamani har na dala Miliyan 600, duk kuwa da zargin keta hakkin bil Adama da ake yiwa Najeriyar.

Jiya Alhamis ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon, ta ce ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta amince da cinikin ta kuma mika batun ga ‘yan Majalisar Dokokin Amurka din, wadanda ke da kwanaki 30 su amince da cinikin.

Yarjejeniyar ta kunshi saidawa Nigeria jiragen yaki samfurin Super Tucano guda 12, wadanda ake amfani da su wajen kai kananan hare-hare.

Ma’aikatar tsaron Amurka ta ce jiragen zasu taimakawa sojojin Najeriya a yakin da suke da kungiyar Boko Haram da kuma ‘yan ta’addar ISIS, zasu kuma taimaka wajen yaki da fataucin miyagun kwayoyi da makamai da kuma safarar mutane.

Jim kadan kafin ya sauka daga mulki ne Tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama ya dakatar da yarjejeniyar cinikin jiragen, biyo bayan wani harin da wani jirgin saman yakin Najeirya ya kai kan sansanin ‘yan gudun hijira dake kusa da iyakar Nigeria da kasar Kamaru, wanda yayi sanadiyar asaran rayukan fararen hula 230 wadanda yakin Boko Haram ya daidaita.

Daga baya ne shugaba Donald Trump ya buga wa shugaba Mohammadu Buhari na Nigeriaya inda ya sanr da shi cewa ya goyi bayan sayarwa da Najeriya jiragen yakin domin ta yaki ta’addanci.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG