Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Fidda 'Yan Takarar Shugaban Kasar Amurka


Taron fidda 'yan Takarar shugaban kasar Amurka na "Iowa Caucus"
Taron fidda 'yan Takarar shugaban kasar Amurka na "Iowa Caucus"

Yau ne ake gudanar da tarukan zaben 'yan takara mataki na farko a jihar Iowa, wanda yake da munimmancin gaske a zaben tsayar da 'yan takarar shugaban kasa a Amurka.

Da sanyin safiyar yau Litinin ne Amurkawa, a jihar Iowa suka fara turuwa zuwa cibiyoyi fiye da 1000 a makarantu da wuraran karatu domin tattaunawa da nuna zabin su game da masu son tsayawa takara ‘yan Republican ko a Democrats.

Yayinda “yan republicans basu da shahararun 'yan takara da zasu kalubalanci shugaba Donald Trump, me neman zarcewa a wa’adin mulki na biyu, hankali ya fi karkarta akan jam’iyyar Democrats wanda ke muradin ta tsai da dan takara da zai fafata da Trump a zaben shekarar nan ta 2020.

Tuni ‘yan takara musamman na ‘yan Democrats suka kamala gangamin karshe a Iowa tare da bayyanawa jamma’a manufofinsu da kuma dalilan da ya sa suke ganin su suka fi cancanta jam’iyyar ta tsai da su takara.

Duk da cewa wasu jama’a sun ruga sun ayyana ‘yan takarar da zasu goyi baya a ransu, wasu da dama na jiran a fara tarukan domin jin alkiblar jama’a da kuma tsare-tsaren ‘yan takarar da suka yi dai-dai da bukatun su a taruka.

Jama’a na da bukatu da kudirori dabam-dabam, amma sha’anin shigowar baki a Amurka, shine babban abin da ya dami dubun dubatan Amurkawa ‘yan asalin kasar Afirka da zasu shiga zaben na Iowa.

Abu mafi mahimmanci a tarukan na yau, wanda akeyi wa lakabi da IOWA CAUCUS a turance, shine zai bayyana zabin jama’a daga cikin ‘yan takara da zaben wakilai wanda kuma za a rarrabawa ‘yan takaran da suka sami hayewa a wannan matakin, domin zaben fitar da gwani na gama gari da za a gudanar a ranar 3 ga watan Maris.

A saurari cikakken rahoton daga Murtala Farouq Sanyinna:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00



Facebook Forum

XS
SM
MD
LG