Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Aiwatar Da Hukuncin Kisa Akan Wasu Mayakan Al Shabab


Wasu mayakan Al Shabab a Somaliya

Kwamandan dakarun Somalia, Farah Mohammed Turba, ya fadawa sashen Somalia na Muryar Amurka cewa, mutanen da aka kashe sun kwashe tsawon watanni biyar a fursuna, suna kuma daga cikin wani gungun mutane da suka kware wajen kisa

Jami’ai a Somaliya da masu fafatukar kare hakkin bil Adama, sun ce sojojin kasar sun kashe wasu mayakan Al-Shabab shida ba tare da an gurfanar da su a gaban kuliya ba.

Kwamandan dakarun Somalia, Farah Mohammed Turba, ya fadawa sashen Somalia na Muryar Amurka cewa, mutanen da aka kashe sun kwashe tsawon watanni biyar a fursuna, suna kuma daga cikin wani gungun mutane da suka kware wajen kisa.

Ya kara da cewa, an kama daya daga cikin mutanen da hanu dumudumu yana kashe wani sojan kasar, kuma cafke shi da aka yi ne ya kai ga kama sauran mutane biyar, sannan daga karshe aka kashe su.

A ranar Lahadi aka harbe mayakan na Al Shabab a garin Bardhere, mai tazarar kilomita 300 daga Mogadishu babban birnin kasar.

‘Yan uwan wadanda aka kashe, da suka tuntubi Muryar Amurka, sun nuna korafinsu kan yadda aka kashe masu ‘yan uwa ba tare da yi masu shari’a ba.

Amma kwamandan dakarun kasar, ya ce su sun bi umurni ne da Ministan tsaron kasar ya ba su.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG