Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Amince Da Kasafin Kudin Da Ya Sa Aka Bude Ma'aikatun Gwamnatin Amurka


Majalisar dokokin Amurka da safiyar yau Juma'a a lokacin da aka amince da kasafin kudi
Majalisar dokokin Amurka da safiyar yau Juma'a a lokacin da aka amince da kasafin kudi

Majalisar wakilai ta amince da kasafin kudin da zai bar ma'aikatun gwamnati a bude har zuwa ranar 23 ga watan Maris.

Majalisar wakilan Amurka ta amince da matsayar da aka cimma ta gagarumin kasafin kudi mai yawan dala biliyan 400 da safiyar yau Juma’a, da nufin kawo karshen dan takaitaccen rufe ma’aikatun gwamnatin kasar da aka yi.

‘Yan majalisun, sun kada kuri’a ne, inda 240 suka amince da kasafin yayin kuma da 186 suka zabi akasin hakan.

Wannan mataki kuma na nufin yanzu an mika kasafin kudin ga shugaban kasa Donald Trump domin ya rattaba hanu akai.Sai dai, wannan kasafin zai kare ne a karshen a ranar 23 na watan Maris.

Yanzu ‘yan majalisar sun samu damar wannan takaitaccen lokaci, domin su tsara yadda za a kashe kudaden na sauran zangon wannan shekara da zai kare a ranar 30 ga watan Satumba.

Wasu ‘yan siyasa, sun nuna adawarsu da wannan kasafin kudi wanda suka ce an kara adadinsa, ba tare da an samar da kariya da wasu bakin haure sama da miliyan daya da ba su da takardun izinin zama a Amurka ba, wadanda aka fi kiransu da “Dreamers” a turance.

Gabanin daukan wannan matsaya ta amincewa da kasafin kudin, aka rufe ma’aikatun gwamnati na dan takaitaccen lokaci yayin da ‘yan majalisar suka gaza kaucewa wa’adin da kudaden gwamnati za su kare.

Wannan shi ne karo na biyu cikin kasa da wata guda, da ake rufe ma’aikatun gwamnatin na dan wani takaitaccen lokaci.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG