Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ayyana Dokar Ta Baci a Yankin Da Aka Kashe Faransawa a Nijar


Shugaba Mahamadou Issoufou
Shugaba Mahamadou Issoufou

Sakamakon harin da ya yi sanadin mutuwar ’yan Nijar 2 da Faransawa 6 a kauyen Koure na yankin Tilabery, Majalisar Tsaron Jamhuriyar Nijar ta bada sanarwar kafa dokar ta baci a gundumomin Kollo da Balleyara.

An yi hakan ne da nufin magance matsalar tsaron da ake fama da ita akan iyakar kasar da kasashen Mali da Burkina Faso.

Kamar yadda aka saba a duk lokacin da wani muhimmin abu mai nasaba da sha’anin tsaro ya wakana a kasar, a wannan karon ma Shugaba Issouhou Mahamadou ya jagoranci zaman taron Majalisar Tsaron Kasa wato conseil national de securite a fadarsa.

Bayan nazarin halin da ake ciki a yau biyo bayan harin garin Koure majalisar ta yanke shawarar kafa dokar ta baci a gundumomin Kollo da Baleyara dake yankin Tilabery.

Wani dan kungiyar kare hakkin jama’a ta Sauvons le Niger, Salissou Amadou ya shaida wa Muryar Amurka cewa a ganinsa "wannan matakin ya yi daidai, ko da yake samun nasarar abinda aka sa gaba ya danganta ga yanayin mu’amular jami’an tsaro da al’umma."

Duk da yake wasu rahotanni na cewa dakarun tsaron da suka bi sawu sun yi nasarar fatattakar ‘yan bindigar da suka kai hari a karkarar yawon bude ido ta Koure, da alama abin na ci gaba da sosa ran jama’ar Nijar yanzu haka.

Tun a shekarar 2017 hukumomi suka kafa dokar ta baci a yankunan Diffa da wani bangare na yankin Tilabery da na Tahoua sakamakon yawaitar ayyukan kungiyoyin ‘yan ta’adda, to amma la’akari da sabon salon da ‘yan bindiga suka bullo da shi, ya sa Majalisar Tsaro ta Kasa fadada abin zuwa gundomin Kollo da Balleyara, inda daga yanzu za a takaita zirga-zirga.

Saurari cikakken rahoton Souley Barma a cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG