Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An bada Izinin Kama tsohon shugaban kasar Panama Ricardo Martinelli


Tsohon shugaban kasar Panama, Ricardo Martinelli

A kasar Panama kotun koli ta bayar da izinin kama tsohon shugaban kasar Ricardo Martinelli, domin ya fuskanci tuhumar da ake masa na leken asirin ‘daruruwan mutane ba tare da izini ba ko ince ba bisa doka ba.

Ana zargin tsohon shugaban kasar ne da kutsawa cikin bayanan mutane sama da 150 alokacin da yake shugabanci, ciki harda sauraron hirar mutanen ta waya da karanta sakonnin karta kwana. Martinelli dai zai fuskanci tuhuma kan laifuffuka da dama alokacin da yake kan mulki, ciki harda yin amfani da kudade ba bisa ka’ida ba. an kuma kwace rigakafin da aka yi masa saboda shine shugaban jam’iyya.

Tsohon shugaban mai shekaru 63 da haihuwa, ya arce daga kasar Panama a farkon shekarar nan kuma ana kyautata tsammanin yana zaune yanzu haka a birnin Miami ta Amurka, ya ki amincewa da tuhumar da ake masa a wata wasika da aka kafe kan yanar gizo a farkon watannan, yana cewa shugaban kasar na yanzu na son ya tsananta masa ne kawai.

XS
SM
MD
LG