Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsoffin Fursinoni a Jihar Virginia Sun Sami Damar Ci Gaba Da Yin Zabe


Gwamnan jhar Virginia Terry McAuliffe.
Gwamnan jhar Virginia Terry McAuliffe.

Gwamna Terry McAuliffe ne ya yiwa fursinoni su kusan dubu metan wannan afuwa ranar jumma'a.

A jihar Virginia dake nan Amurka makwabciyar nan birnin Washington DC, hukumomi sun maidowa tsoffin fursinoni su kimanin dubu metan, 'yancin yin zabe.

Gwamnan jihar, dan jam'iyyar Democrat Terry McAuliffe, ya sanya hanu kan dokar gwamna, waccce ta sake baiwa tsoffin fursinonin 'yancin yin zabe, bayan da suka kammala zaman sarka.

"Na bukaci a bani dalili daya, ta yadda al'uma take amfana da kyale dubun dubata 'yayanta a dabaibaye tamkar bayi. Hakika babu wata hujja ta fuskar doka walau ta hankali, na ci gaba da haka," inji Gwamna McAuliffe.

Masu sukar lamirin matakin, sun ce Gwamnan ya dauki wannan matakin ne domin dalilai na siyasa, suna masu cewa hakan zai kara yawan masu goyon bayan jam'iyyar Democrat, a zaben shugaban kasa da za'a yi cikin watan Nuwamban bana.

Tilas tsoffin fursinoni wadanda wannan afuwar ta shafa, suyi rijista kamin suyi zabe, kuma ana ji masu rajin kare 'yancin zabe zasu basu cikin jihar domin su yiwa wadannan mutane rijista.

XS
SM
MD
LG