Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bankado Ma’aikatan Bogi Har 12,609 A Jihar Adamawa


Jihar Adamawa
Jihar Adamawa

Gwamnan jihar Adamawa Sanata Mohammadu Bindo Umaru Jibrilla yayi bayani game da ma’aikatan bogi da aka bankado a jihar.

Watanni Goma sha Daya da suka gabata ne gwamnatin jihar Adamawa ta kafa wasu kwamitoci guda biyu domin binciken ma’aikatan kananan hukumomin jihar, binciken kuwa da ya bakado ma’aikatan bogi kusan Dubu 12,609.

Ahmed Sajo dake zama sakataren yada labaran jihar, yace abin mamaki ne ma ga wasu abubuwan da kwamitin suka gano. Inda yace alokacin da ‘yan kwamitin suke mika musu rahoto sun tabbatar da cewa am sami badakala dayawa.

Ba tun yau bane dai kungiyar kwadago a jihar ke kokawa kan abin da ta kira shakulatun bangaro da halin da ma’aikatan jihar ke fama da shi, batun ma da shugaban kungiyar kwadago a jihar Kwamarad Dauda Maina, ke cewa zasu saka ido domin yadda zata kaya game da wannan danbarwar ma’aikatan bogi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00

XS
SM
MD
LG