Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bankado Ma’aikatan Bogi Har 600 A Jihar Neja


Wasu ma'aikata ke kallon wutar da ta tashi a bututun mai a jihar Neja.

Kimanin ma’aikatan bogi 600 ne gwamnatin jihar Neja tace ta bankado a wani binciken kwa kwaf da gwamnatin jihar ke yiwa ma’aikatanta a halin yanzu.

Gwamnatin Neja dai tace ta dauki matakin binciken ma’aikatan ne domin bankado cin hanci da yayi katutu a tsakanin ma’aikatun gwamnatin jihar.

Gwamnan jihar Alhaji Abubakar Sani Bello, ya bayyana cewa aikin tantance ma’aikata da ake yi a halin yanzu, sakamakon binciken ya nuna akwai gagarumin cin hanci da al’mundahana da aka bankado.

To sai dai a nata bangaren kungiyar Kwadago ta jihar Neja ta nuna rashin gamsuwa da yadda aikin tantance ma’aikatan ke tafiya. Shugaban kungiyar reshen jihar Neja, Kwamarad Idris Ndaku, yace matsalar ma’aikata itace matsalar su, kuma basu amince ba da yadda gwamnan ke takuwa ma’aikata ba.

Haka zalika kungiyar Kwadagon tace tana da shakku kan yawan adadin ma’aikatan bogin da akace an bankado a sakamakon.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00
Shiga Kai Tsaye

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG