Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bankado 'Yan Leken Asirin Amurka


Wani dan sandan Lebanon yana nunawa 'yan jarida kayan da yace an samu daga hannun wasu mutanen da ake zargin cewa 'yan leken asirin Isra'ila ne da aka bankado su, a watan Mayun 2009.
Wani dan sandan Lebanon yana nunawa 'yan jarida kayan da yace an samu daga hannun wasu mutanen da ake zargin cewa 'yan leken asirin Isra'ila ne da aka bankado su, a watan Mayun 2009.

Iran da kungiyar Hezbollah ta Lebanon sun bankado wasu 'yan leken asirin Amurka, har ma an kashe wasu daga cikinsu

Fadar shugaban Amurka ta White House ta ki yarda ta ce uffan game da rahotannin dake cewa an bankado gungu-gungun ‘yan leken asirin Amurka a Iran da Lebanon, a wani lamarin da zai kasance mummunar koma-baya ga ayyukan leken asirin Amurka a wadannan kasashe.

Kakakin fadar White House, Jay Carney, ya fadawa ‘yan jarida jiya litinin cewa ba zai yi sharhi kan batutuwan da suka shafi leken asiri ba. Amma a can wani gefen dabam, jami’an gwamnatin Amurka sun tabbatarwa da ‘yan jarida cewa da gaske ne Iran da kuma kungiyar Hezbollah ta Lebanon sun bankado wasu ‘yan leken asirin Amurka. Jami’an suka ce an kashe da yawa daga cikin ‘yan leken asirin, yayin da wasu ke cikin hatsarin mutuwa.

‘Yan leken asirin su na aiki ne ma Hukumar leken Asirin Amurka ta CIA, kuma su na taimakawa Amurka wajen tattara bayanai game da shirye-shiryen nukiliya na kasar Iran da kuma ayyukan kungiyar Hezbollah, wadda Amurka ta ke dauka a matsayin kungiyar ta’addanci.

Wasu jami’an sun ce bankado dan leken asiri na daya daga cikin hadarurrukan dake tattare da wannan sana’a. Amma wasu jami’an da suka san abinda ya faru a wannan lamarin sun ce akwai alamun cewa hukumar leken asirin Amurka ta CIA ta kasa daukar matakan da suka kamata na tabbatar da lafiyar masu yi mata leken asiri a kasashen.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG