Accessibility links

An Bayyana lambobin Tambola Na Dala Milyan 640

  • Aliyu Imam

Alamar Tambola Na Magudan kudi.

A can cikin daren jiya jumma’a aka bayyana lambobin tambola ta samada dala milyan dari 640 da aka sayar a daya daga cikin jihohin Amurka .

A can cikin daren jiya jumma’a aka bayyana lambobin tambola ta samada dala milyan dari 640 da aka sayar a daya daga cikin jihohin Amurka .

Kwadayin cin wadan nan magudan kudi watau rabin dala milyan dubu daya, yasa mutane shiga layi na sa’o’I a fadin jihohin Amurka 42, da gundumar Columbia da tsibiran Amurka da ake kira Virgin islands.

Mutuminda ko mutanenda suka sami nasara kuma suke so a biya su nan take, zasu karbi dala milyan 462, ko kuma a biya su kaso-kaso a duk shekara har su karbi kudaden baki daya dala milyan 640. Amma za’a cire harajin jiha da gwamnatin tarayya.

Magudan kudaden sun taru ne saboda babu wanda ya sami nasara a tambaolar da aka yi cikin watan janairu, da wadanda suka biyo baya kamar sau 18 da aka yi.

XS
SM
MD
LG