Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bude Cibiyar Bincike Kan Coronavirus a Kaduna


Pascal Strupler, babban daraktan ma'aikatar lafiya a Switzerland bayan da ya gama jawabi kan matakan kare kai daga cutar Coronavirus.
Pascal Strupler, babban daraktan ma'aikatar lafiya a Switzerland bayan da ya gama jawabi kan matakan kare kai daga cutar Coronavirus.

Yayin da jihohi da dama a Najeriya ke ta kokarin shirye-shiryen tunkarar yiwuwar shigowar cutar Coronavirus, bayan da aka samu mutum daya mai dauke da ita a Jihar Legas, Kaduna ma ta bi sahunsu.

Gwamnatin Jihar ta Kaduna ta bude wata cibiyar gudanar wa ta aikin gaggawa.

Cibiyar dai matattarar tara bayanai ce game da duk wani rahoto kan wannan cuta ta Coronavirus, wacce kwararru za su dinga tattauna wa don su tattance bayanan da suka tattara.

Amma dai Jami’ar hulda da jama’a ta ma’aikatar lafiya a Kaduna Mrs Rose, ta sheda wa Muryar Amurka cewa cibiyar ba wurin kwantar da wadanda aka samu da cutar ba ne ba.

A cewarta “ wuri ne da masu ruwa da tsaki za su dinga tattara bayanai kan duk wani sabon labari da aka samu kan cutar, domin shirya yadda za a tunkare ta, idan an samu bullarta.”

Mrs Rose dai ba ta bayyana unguwar da cibiyar take a Kaduna ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG