Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bude Rumfunan Zaben Shugaban Kasar Togo


Faure Gnassingbe
Faure Gnassingbe

Zaben kasar Togo na tafiya tunda har an bude rumfunan zabe shugaban kasa inda a cikin 'yan takarar har da shugaban kasa mai ci yanzu da yake neman ta zarce karo na uku.

A yau asabar an bude rumfunan zabe a kasar Togo na zaben shugaban kasa. Shugaban kasar mai ci a yanzu Faure Gnassingbe na neman tazarcen karo na 3 wanda in ya samu zai zama iyalan gidansu ke mulkar kasar kusan shekaru 50.

Ya dai dare karagar mulki ne a shekarar 2005 bayan mutuwar mahaifinsa Gnassingbe Eyadema wanda ya mulki kasar tsawon shekaru 38. Shima Jean-Pierre Fabre da ya taba fitowa takara a zaben da ya gabata ana sa ran zai zo na biyu a zaben tashin farko na zaben shugaban kasa.

Masu rajin kare hakki sun soki Togo da amfani da karfin tuwo akan masu zanga-zanga. Daruruwan masu sa ido sun sauka a Togo don ganewa idanunsu yadda zata kaya a zaben da ake sa ran masu kada kuri’a Miliyan 3 da rabi ne da zasu wakilcin rabin yawan jama’ar kasar.

XS
SM
MD
LG