Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bude Taron Kungiyar AU Na Kwana Uku A Birnin Accra

Taron Kungiyar AU Na Kwana Uku A Birnin Acccra
Taron Kungiyar AU Na Kwana Uku A Birnin Acccra

An bude taron AU domin tattauna batun juye-juvenile mulki a Afirka inda shugaban kungiyar ECOWAS Nana Alofi Ado ya yi toffin Allah ya tsine akan yadda wasu kasashen Yamma ke tsoma baki bisa harkokin cikin gidan wasu kasashe a Afirka.

ACCRA, GHANA - Shugaban ya ce wasu kasashen na Yamma na da hannu a juye juyen mulki da ke faruwa a sassan nahiyar Afirka. ya ce suna hakan ne domin cimma manufofinsu.

Taron Kungiyar AU Na Kwana Uku A Birnin Acccra
Taron Kungiyar AU Na Kwana Uku A Birnin Acccra

Shugaban na Ghana ya fadi hakan ne a taron kwana uku na kungiyar AE tare da hadin guiwar gwamnatin Ghana a birnin Accra inda taron ya maida hankali akan juye juyen mulki ba kan ka’ida ba da nahiyar ke fama da ita.

Ya ce suna kushe gwamnatocinsu da aka kafa ta dimokradiyya tare da cusa wa al’ummar kasashen akidar aiwatar da zanga-zangar adawa da gwamnati.

Taron Kungiyar AU Na Kwana Uku A Birnin Acccra
Taron Kungiyar AU Na Kwana Uku A Birnin Acccra

Shugaban ya kuma tabo matakan da AU da ECOWAS din ke dauka na yin Allah wadai da juyin mulki, ya ce hakan kadai ba zai haifar da wani alheri ba sai dai idan aka dauki matakan ladabtar da wadanda suka jagoranci juyin mulki.

Taron Kungiyar AU Na Kwana Uku A Birnin Acccra
Taron Kungiyar AU Na Kwana Uku A Birnin Acccra

Ya kuma kara da cewa kungiyoyin na AU da ECOWAS ya kamata su ladabtar da shugabannin da ke yi wa tsarin mulki kwaskwarima domin yin ta zarce.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti daga Hamza Adams:

An Bude Taron Kungiyar AU Na Kwana Uku A Birnin Acccra
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00

Hira Da Dakta Faruk Bibi Faruk Akan Matsalar Tsadar Rayuwa A Najeriya Kashi Na Biyu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG