Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Burkina Faso Ta Nada Gwamnatin Wucin Gadi Bayan Juyin Mulki


Paul-Henri Damiba da Albert Ouedraogo
Paul-Henri Damiba da Albert Ouedraogo

Shugaban Burkina Faso na wuccin gadi, Paul-Henri Damiba ya amince da kafa sabuwar gwamnati da ta hada da ministan tsaro wanda shi ne ma ministan tsaron a gwamnatin tsohon shugaban kasar, Roch Kabore kafin a hambarar da shi a wani juyin mulkin da sojoji suka yi.

A ranar Laraba ne aka rantsar da Damiba a matsayin shugaba na wuccin gadi na tsawon shekaru uku, bayan da ya jagoranci tawagar hafsoshi wajen hambarar da Kabore a watan Janairu.

Sabuwar gwamnatin mai ministoci 25 ta hada da ministan tsaro Janar Barthelemy Simpore, wanda ya ci gaba da rike mukamin da ya rike a karkashin Kabore, a cewar sanarwar umurnin.

A ranar Alhamis ne aka sanar da nadin masanin tattalin arziki Albert Ouedraogo a matsayin Firaministan wuccin gadi na kasar.

Juyin mulkin sojan Burkina Faso shi ne karo na hudu a yammacin Afirka cikin watanni 18, bayan da yi biyu a Mali da kuma daya a Guinea.

Yanzu haka sabbin hukumomin za su yi kokarin shawo kan munanan hare-haren masu kishin IS da suka mamaye yankunan kasar Burkina Faso wanda hakan ya haifar da nawaya ga albarkatun kasa kalilan da kasar ke da su.

~ REUTERS

XS
SM
MD
LG