Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Anyi Bikin Bude Wasannin Olympics A Brazil


Rio Olympics

An kiyasin mutane bilyan uku ne suka kalli bikin bude wasannin ta talabijin.

An yi bikin bude gasar motsa jiki na Olympics a birnin Rio na Brazil, inda dubun dubatan jama'a suke sowa, aka rera wakar da take bayyana kauna ga Brazil.

Ana kiyasin mutane milyan dubu uku ne suka kalli bikin bude wasannin da aka yi jiya jumma'a, inda kungiyoyi 'yan wasa daban daban 200, ciki harda tawaga irinta ta farko ta 'yan gudun hijira, da suka dunkule wuri daya suma za'a kara da su.

Tawagar 'yan gudun hijirar ta hada da 'yan wasa 10 daga kasashen Sudan ta kudu, da Habasha, da Jamhuriyar Demokuradyyar kwango, da Syria, wadanda kwamitocin wasannain Olympics na kasashe da suke zaman gudun hijira suka zabe su, kasashen sune Kenya, da Luxemberg, da Brazil, da Belgium, da Jamus. Tawagar data kunshi maza shida da mata 4, zata shiga wasannin gudun tsere, da dambe ko kokawa, da nunkaya.

Wasan wuta da 'yan raye raye masu yawa saye da kayayyaki masu daukar ido, wanda ya kunshi kishi ko zakalkalewar da aka san Brazil da shi sun kayatar.

XS
SM
MD
LG