Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bude Wata Hanya Da Aka Rufe Kusan Shekaru 3 Dalilin Boko Haram A Maiduguri


Hafsan Sojojin Najeriya Tukur Yusuf Buratai

A karshen makon nan ne dai babban Hafsan Rundunar Sojojin Kasa na Najeriya, Lt Janal Tukur Buratai, ya bude wata hanya da ta tashi daga garin Maiduguri ta kuma hada jahohin Adamawa da Taraba da kuma jihar Gombe, da aka rufe fiye da shekaru uku da suka gabata sakamakon tsaro da hare haren da yan Boko Haram ke kaiwa.

Bude wannan hanya dai yasa jama’a sun fara zirga zirga, wanda a baya su kanyi zagaye ne mai nisan gaske, tun dai lokacin da jami’an tsaro suka hana bin hanyoyin ne dai ‘Kauyukan da ke kan hanyar suka zama tungar ‘yan Boko Haram, kafin daga baya sojojin Najeriya su fatattake su.

Babban Hafsan Sojan Najeriya ya bi wannan hanya tare da tawagarsa don nunawa jama’a cewa yanzu haka an bude wannan hanya a hukumance. Kuma jama’a na iya bin hanyar duk lokacin da suka ga dama.

Wakilin Muryar Amurka Haruna Dauda, ya ziyarci daya daga cikin tashoshin mota da ake kira Tashar Kano a cikin garin Maiduguri, inda yaji ra’ayoyin direbobi da fasinjoji. Yawancin mutanen dake wannan Tasha sunyi matukar farin ciki da bude wadannan hanya.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:49 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG