Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun ba da sanarwar sake bude wuraren ibada a fadin kasar daga yau 13 ga watan Mayu.
Hakan dai ya nuna yadda ake sassauta dokar hana fitar dare da aka kafa a birnin Yamai jim kadan bayan da aka samu bular annobar cutar Coronavirus a tsakiyar watan Maris din da ya gabata.
Baya ga haka za a sake bude makarantu a ranar 1 ga watan Yuni mai zuwa.
A karshen wani taron da ya hada hukumomi da shuwagabanin addinai da kuma kwararru a fannin yaki da cutar wanda aka gudanar a birnin Yamai ne bangarorin suka yanke shawarar sassauta wasu daga cikin matakan da gwamnati ta dauka domin takaita yaduwar cutar.
Hukumomin sun sanar cewa mutane za su iya halartar wuraren ibada a ko ina a fadin kasa amma da sharadin mutunta matakan kariya.
A dai bangare gwamnatin ta Nijar ta kuma ba da sanarwar kawo karshen dokar hana fitar dare da aka kafa a birnin Yamai wadda ta yi watanni kusan biyu tana aiki.
Sanarwar ma’aikatar lafiya ta kasar ta yi nuni da cewa an gano karin mutum 22 da suka kamu da wannan cuta a daren jiya Talata.
Daga cikin mutum 854 da suka harbu da cutar kawo yanzu mutane 648 ne suka warke yayin da 159 ke kwance a asibiti sai wasu 47 da suka rasu sanadiyar cutar ta COVID-19.
WASHINGTON D.C. —
Yaran Da Boko Haram ta Kashe Iyayensu Sun Samu Gata a Sokoto
Maris 04, 2021
Yaran Da Boko Haram ta Kashe Iyayensu Sun Samu Gata a Sokoto
Rayuwar Birni
Fabrairu 28, 2021
Rayuwar Birni – Dan Kasuwar Gwari A Abuja
Za ku iya son wannan ma
-
Maris 07, 2021
Za Mu Kotu Don Kalubalantar Sakamakon Zabe - Mahamane Ousman
-
Maris 04, 2021
Kotun Kolin Ghana Ta Tabbatar Da Sake Zaben Akufo-Addo
Facebook Forum