Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bukaci A Bi Digdigin Yadda Miyagun Kwayoyi Ke Shiga Kano


Miyagun kwayoyi
Miyagun kwayoyi

Mhalarta taron da aka shirya akan dabarun dakile shigowa da miyagun kwayoyi sun bukaci a bi digdigin yadda kwayoyin ke shigowa Kano da ma Najeriya gaba daya.

Alhaji Aminu Buba babban jami'in dake kula da yankin arewacin Najeriya na kungiyar NFRP yayi karin haske dangane da kudurorin da aka cimma a taron.

Na farko jami'an hukumar dake yaki da safara da shan miyagun kwayoyi bata da iasassun ma'aikata a jihar Kano da zasu sa ido koina har su cafke masu aikata laifin safarar kwayoyi. Wajibi ne hukumar ta kara jami'ai.

Ya kira a yi hadin kwai da kungiyoyi da jama'a da sarakuna domin a yaki wannan annobar da ta addabi jihar.

Mataki na biyu shi ne wayar da kawunan iyaye akan illar shan wadan nan miyagun kwayoyin. Ya alakanta shan miyagun kwayoyi da tabuwar hankali musamman a birane kamar Kano.

Samfurin miyagun kwayoyi
Samfurin miyagun kwayoyi

Ya kamata a duba dokokin kasar akan yaki da muggan kwayoyi. Akwai wasu kwayoyi da doka bata yi masu tanadi ba, wato kamar solution da sauransu.

Kazalika jami'in yace kungiyar NFRP zata cigaba da aiki da sauran hukumomi da kungiyoyi domin yaki da safarar miyagun kwayoyi.

Zasu gabatar da kudurorin wa gwamnan jihar da mai martaba sarkin Kano Alhaji Muhammad Lamido Sanusi II.tare da ganawa da wasu masu ruwa da tsaki na jihar domin yadda za'a yi aiki da shawarwarin da aka cimma a taron.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00
Shiga Kai Tsaye

Zaben 2023

TASKAR VOA: Yadda Masu Fama Da Larurar Gani Za Su Kada Kuri’a A Zaben Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG