Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bukaci Masu Shirin Komawa Raqqa a Syria da Su Dakata Yin Hakan


Wani bangaren birnin Raqqa

Kwana kwanan nan aka kwato birnin Raqqa daga hannun mayakan ISIS amma akwai dubban nakiyoyi da aka binne saboda haka hadari ne mutane su koma birnin yanzu, sai su dakata har sai an kakkabe bama baman.

An bukaci ‘yan kasar Syria da ke da burin komawa Raqqa bayan da aka kubutar da birnin daga hannun mayakan kungiyar IS, da su dakata har sai baba ta gani.

Gamayyar jami’an sojan kasa-da-kasa, ta ce matsalar ita ce akwai dubban bama-bamai hadin gida, da tarkuna da suke baje a Birnin, inda tuni wasunsu suka fara salwantar da rayuka.

“Tuni mun fara samun rahotannin mutuwar fararen hula daga wadanda suka yi kokarin komawa.” In ji kwamandan dakarun hadin gwiwa na musamman, Manjo Janar James Jarrard a jiya Talata, yayin wani jawabi da ya yi wa manema labarai a Bagadaza, daga ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon.

Kungiyoyin ba da agaji, sun yi kiyasin cewa sama da mutane dubu 200 ne suka tsere daga birnin na Raqqa, tun bayan da fafatukar kwato birnin ta zafafa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG