Accessibility links

Amurka Ta Shawarci Shugaba Wade Na Senegal kar Ya Sake Takara

  • Jummai Ali

Shugaba Abdoulaye Wade na Senegal, lokacinda da yake gabatar da jawabi gaban baban taron Majalisar Dinkin Duniya.

Wakilan Majaliar dokokin Amirka sun bukaci shugaba Abdoulaye Wade da aka ya sake neman wani wa'adin mulki, a zaben da za'a yi a kasar badi idan Allah ya kaimu.

Wasu wakilan Majalisar dokokin Amirka guda hudu, sun bukaci shugaba Abdoulaye Wade na Senegal, da kada ya sake neman wani wa'adin mulki, a zaben da za'a yi a kasar badi idan Allah ya kaimu.

A wata wasika da suka rubuta, wadda sashen Faransanci na Muryar Amirka ya samu, wakilan Majalisar dattijai guda biyu da wasu wakilan Majalisar wakilai guda biyu sun lura da irin agangamomin da aka yi a titunan baban birnin kasar Senegal a farkon wannan shekara, a saboda haka sun fadawa shugaba Wade cewa tana yiwuwa an samu karin hargitsi a kasar idan yace zai sake tsayawa takara.

Sunyi kashedin cewa rikicin tsarin mulki tana iya dagula ci gaba ko kuma yunkurin da ake yi na kafa mulkin democradiya a kasar, kuma daukan irin wannan mataki yana iya raunana dangantaka tsakanin Amirka da Senegal.

Shugaba Wade, wanda yanzu shekarunsa na haihuwa tamanin da biyar ne, tuni yayi wa'adin mulki biyu, kamar yadda tsarin mulkin kasar ya tanada. To amma kuma duk da haka magoya bayan Mr Wade sunce yana iya sake tsayawa takara, domin a lokacinda ya fara tsayawa takara a shekara ta dubu biyu, ba'a fara amfani da tsarin mulkin ba.

Har yanzu dai kotun tsarin mulki ta kasar bata yanke hukunci akan cancantarsa.

Idan aka kwatanta da sauran kasashen Afrika akwai zaman lafiya a Senegal, to amma masu sukar lamirinsa, sun zargi shugaba Wade da laifin kara zama mai mulkin kama karya.

Masu hamaiya da shugaba sunce an dauki wannan mataki ne da nufin ganin cikin sauki an sake zaben shugaba Wade ko kuma dansa Karim Wade ya gaje shi.

XS
SM
MD
LG