Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bukaci Shugaba Donald Trump Da Ya Gabatar Da Shaida


Donald Trump

Kwamitin da ke kula da harkokin leken asiri a majalisar Amurka ya bukaci Shugaban kasa Donald Trump da ya gabatar da shaida a ranar litinin wacce ta nuna anyi satar sauraren waya a Trump Tower.

Shugaban kasar ya yi babatu a Twitter satin da ya gabata cewa tsohon shugaban kasa Barack Obama yasa anyi satar sauraran wayar , amma Trump bai bada wata shaida ba kan afkuwar hakan. Trump ya rubuta a Twitter cewar “Babu dadi, yanzunnan na gano Obama yasa anyi satar sauraron waya a Trump Tower, kafin nasararmu. Babu abinda suka gano . Wannan Kagene.”

Shugaban kwamitin Devin Nunes, Dan Jam’iyyar Republican daga California, da kuma Adam Schiff shima daga California wanda yake mai babban mukami a kwamitin na Demokrat, sun tura wasika zuwa ga Trump don bukatar shaida domin karawa zargin satar sauraron wayar karfi.

Mai Magana da yawun tsohon shugaban kasa Barack Obama yace, Zargin da Trump yake karyace kawai.

Trump dai baice komai dangane da batun satar sauraron wayar ba tun bayan rubutun da yayi a twitter.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG