A wani taron manema labarai da kungiyar ta kira a Lagos ta zargi babban Bankin da kin baiwa kanfanonin cikin gida damar samun kudaden kasashen wajen domin sayo kayan aiki daga ketare, a maimakon haka sai kanfanonin kasashen waje ake baiwa kudaden musaya, su kuma suke karya kanfanonin cikin gida.
Cif Eric Emeolia, dake zama shugaban kungiyar kamfanonin cikin gida, yayi karin haske game da bukatun nasu inda yace, “abin da mukeso gwamnatin Najeriya ta gane shine cewar akasarin wadanda aka nada kama daga shugaban Bankin kasa zuwa ministoci, ba dukkanin sune keda kishin taimakawa gwamnati dama kasa ba, akasarin abin da suke yi baya taimakawa shugaba Buhari wajen ciyar da kasa gaba, don haka ya kamata a sauke su ko kuma dai a sake lale.”
Wannan kira da kungiyar tayi yazo ne a dai dai lokacin da aka ruwaito shugaban kasa Muhammadu Buhari yana kira ga yan Najeriya dasu rungumi amfani da kayan gida domin ciyar da aksar gaba a wajen wani taron tattalin arziki dake gudana a Abuja.
Barrista Faruk Abdullahi shine babban sakataren wannan kungiya, kuma yayiwa wakilin Muryar Amurka Babangida Jibrin karin haske game da manufar su inda yace ana ‘daukar kudaden su ana baiwa baki.
Duk da kokarin jin ta bakin kakakin Babban Bankin na Najeriya yaci tura, sai dai a kwannan nan an rawaito gwamnatin Najeriya tana jaddada goyon bayan ta ga Gwamnan babban Bankin, a tsarin ta na musayar kudaden kasashen waje, wanda kamfanonin cikin gidan ke kuka dashi. Haka itama Bankin kasar ta musanta zargin da ake mata na fifita kamfanonin kasashen ketare akan na cikin gida.
Saurari cikakken rahotan Babangida jibrin daga Lagos.