Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bukaci 'Yan Nijar Dasu Yiwa Kasar Addu'a: Briji Rafini


Firayim Ministan Nijar, Briji Rafini

Jama'ar kasar Nijar na da kyakkyawan fata ga kasar na karuwan arziki darajan zagayowar watan Ramadan

Firayim Ministan Nijar Briji Rafini yayi kira ga 'yan Nijar da suyi addu'o'i domin samun zaman lafiya dawamamiya albarkacin watar azumin Ramadan.

Ya bayana haka ne jim kadan bayan da majalisar koli ta malaman kasar ta bada sanarwar ganin watan azumin Ramadan.

Yana mai cewa kasar na bukatar addu’ar ‘yan kasa domin karuwar arzikin da zaman lafiya maidorewa da kuma samun damuna mai albarka.

A na sa bangaren daya daga cikin Malaman addinin Islaman kasar Malam Jihadi, yace dukkan ibadah da dan Adam ya aikata tashi ce , abin nufi shine duk abinda mutun ya aikata na aikin ibadah akwai abinda aka sheda a fili cewa shine sakamakon bawa, amma azumin watan Ramadan Allah ya boye sakamakon da zai baiwa mai azumi wannan tsakanin bawa da mahallincinsa ne.

A nasu bangaren ‘yan kasuwa sun ce farashin kayayyaki babu laifi sai dai akwai wasu kayayyakin da ba a samun su yanzu haka a kasuwanni in ji wani dan kasuwa me suna Malam Tasiu.

Jama’ar kasar ta Nijar, dai na ci gaba da nuna kyakkyawan fata game da sagayowan watan Azumin Ramadan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

Facebook Forum

Yaran Da Boko Haram ta Kashe Iyayensu Sun Samu Gata a Sokoto

Yaran Da Boko Haram ta Kashe Iyayensu Sun Samu Gata a Sokoto
please wait

No media source currently available

0:00 0:05:31 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Rayuwar Birni

Rayuwar Birni – Dan Kasuwar Gwari A Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00
Karin bayani akan Rayuwar Birni
XS
SM
MD
LG