Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cafke Masu Karkata Kayan Abincin 'Yan Gudun Hijira a Bauchi


Kayan abincin 'yan gudun hijira da aka kama
Kayan abincin 'yan gudun hijira da aka kama

Dubun wasu masu karkata akalar kayayyakin abincin 'yan gudun hijra ta cika a jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya.

An kama wasu mutane da suka sauya akalar kayan abincin da aka ware domin 'yan gudun hijira a Bauchi

Kayan abincin an dauko su ne daga Kaduna zuwa Bauchi duk da cewa akwai rubutun da ke cewa ba na sayarwa ba ne.

An sauke kayan ne a wata Unguwa a Bauchi inda aka fara sauya buhunan abincin zuwa na kasuwa, abin da ya sa mutanen unguwar suka farga suka kuma koka.

Malam Umar Musa Shehu shugaban 'yan gudun hijira na jihar Bauchi ya ce akwai abincin da aka kawo daga wani yankin yammacin Afirka kuma an rubuta cewa ba na sayarwa ba ne.

Da aka tambayi masu sauya buhun sai suka ce su ma sun saya ne daga Kaduna.

Kawo yanzu dai an mika mutanen hannu 'yan sanda har ma an kama wasu da suka sayo kayan wadanda watakila su ba da bayanan da zai kai ga kama ainihin masu shirya wannan cuwacuwar.

Saurari rahoton Abdulwahab Muhammad domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:31 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG