Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Jagoranci Taron Gaggawa Kan Harkar Tsaro


A lokacin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yake jagorantar taron gaggawa kan tsaro a Abuja
A lokacin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yake jagorantar taron gaggawa kan tsaro a Abuja

Rahotanni daga Najeriya na cewa shugaban kasar Muhammadu Buhari, ya jagoranci wani taron gaggawa, inda aka tattauna kan harkar da ta shafi tsaron kasar.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya jagoranci wani taron gaggawa domin tattauna wa kan batun tsaro a kasar.

Buhari ya bayyana hakan a shafinsa an Twitter yana mai cewa an samu fahimtar juna kan lamarin tsaro da harshen turanci.

"Mun himmatu wajen aiwatar da hanyoyin da za su samar mana da maslaha, ba kawai ta yadda 'yan Najeriya za su kara yarda da mu ba, har ma da tabbatar da cewa hanyoyin sun dore a ko wane irin yanayi." https://twitter.com/MBuhari/status/963042559214936066

Tun da farko, jaridun Najeriya sun ruwaito cewa, dukkanin manyan hafsoshin sojin kasar sun halarci taron tare da babban Sifeto Janar din ‘yan sanda, Ibrahim Idris.

Jaridar Daily Trust, ta ruwaito kamfanin dillancin labaran kasar na NAN, na cewa taron ya fara ne da misalin karfe 11:00 na safe.

Najeriya dai ta na fama da matsalar tsaro, musamman dangane da batun rikicin Boko Haram da ya faro tun daga 2009.

A karshen makon da ya gabata, kungiyar ta saki wasu malaman jami’ar Maiduguri da ke jihar Borno da kuma wasu matan ‘yan sanda 10 da kungiyar ta jima tana garkuwa da su.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG