Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cafke Mutane 4 Da Ake Zargi Da Hada Hannu Wajan Kisan Mutane 84 A Faransa


Masu gabatar da kara a Paris, sun ce mutumin nan da ya abka da wata babbar mota cikin cincirindon masu shagulgulan zagayowar Ranar 'Yancin Kasar Faransa, ko Ranar Bastille a birnin Nice, ya hallaka mutane 84, ya aikata hakan ne da taimakon wasu, kuma da alamar ya shafe watanni ya na shiryawa.

Da ya ke magana da manema labarai jiya Alhamis a Paris, babban birnin kasar Faransa, Francois Molins ya ce bayanan da suka samu na hotuna da binciken da ya yi a wayar salularsa, na nuna cewa tun daga shekarar 2015 ya fara shiri.

Molins ya ce wasu mutane biyar da a yanzu ake zargi sun shiga hannu su na fuskantar mataki na farko na zargin aikata ta'addanci, ciki har da hada baki don aikata kisa da kuma mallakar makamai, da kuma rawar da su ka taka wajen taimakawa mutumin ya aikata ta'addancin na ranar 14 ga watan Yuli.

Ya ce mutane hudu ne ake zargi biyu Faransawa 'yan asalin kasar Tunisiya, da wani dan Tunisiya da wani dan Albaniya, da wata mata mai takardar izinin zama 'yar Faransa da kuma Albaniya a lokaci guda. Hukumomin Leken Asirin Tsaron kasa ba su san da su ba a baya, a cewar kafar labaran Faransa ta AFP.

Mutumin da ya abka da motar, Mohammed Lahouaiej Bouhlel, dan shekaru 31, dan asalin kasar Tunisiya ne da ya zauna a Nice na tsawon shekaru.

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG