Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Jihar Indiana Mai Ra'ayin Rikau Ya Yi Bayani Akan Zaben Su Da Donald Trump


Gwamnan Jihar Indiana Micheal Pence, ‘dan ra’ayin rikau na jamiyyar Republican, wanda shine Donald Trump ya zaba a matsayin wanda zai zama mataimakin shugaban kasa, a jiya Talata ya bayar da dalilan da yasa yake ganin sune suka dace su jagoranci Amurka.

Pence wanda tsohon Dan majilisa ne daga jihar Indiana, dake cikin kudu maso tsakiyar Amurka kana daga bisani ya zamo gwamnan jihar, Yanzu haka yana tare da Donald Trump a wajen gangamin da jamiyyar tayi a Cleveland dake cikin jihar Ohio, inda nan ne aka taba tsayar da sanannen dan jamiyyar Republican din nan Ronald Reagan wanda ya mulki Amurka a cikin shekarun baya, har na tsawon waadi biyu.

Pence dan shekaru 57 da haihuwa yayi jawabin da ya dauki hankulan jama’a a rana ta uku wajen wannan taron, wato kwana guda bayan wakilai suka zabi wanda zai tsaya takara a karkasahin tutar jamiyyar ta Republican.

A cikin jawabin sa wajen taron Pence yace ya shirya fadawa Dubun dubatan Amurkawa ta gidan talabijin cewa gwamnatin da Trump yake fatar ganin ya kafa, ita ce gwamnatin da zata jaddada ci gaban Amurka da Amurkawa, bayan kasar tasha fama da manufofi marasa inganci da mulki mara kyau wanda yasa kasashen duniya suka yi rauni a harkokin Amurka.

Tun a cikin shekarar 1950 wannan ne karon farko da wani hamshakin attajiri wanda bai taba rike ko wane irin mulkamin siyasa ba ace ya zamo dan takara a karkashin duka fitattun jamiyyun nan guda biyu, wato ko dai Republican ko kuma Democrat.

XS
SM
MD
LG