Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An caji wata mace anan Amirka da laifin kokarin taimakon kungiyar Islamic state


Yan kungiyar Islamic state

An caji wata mace wadda ke zaune a birnin Philadelphia mai suna Keonna Thomas da laifin kokarin taimakon yan yakin sa kan kungiyar Islamic State

Jiya Juma'a aka caji wata mace wadda take zaune a birnin Philadelphia jihar Pennslyvania nan Amirka mai suna Keonna Thomas wadda kuma ake cewa Fatayat Al Khalifah, da laifin kokarin baiwa kungiyar yan yakin sa kan Islamic state taimako. Wannan shine al'amari na biyu dake da alaka da ta'adanci a kasar Syria daya danganci wata baamerkiya.
Lauyan gwamnati yayi bayanin cewa Keonna Thomas yar shekara talatin da haihuwa tayi kokarin zuwa wata kasar waje domin ta taimakawa kungiyar Islamic State wajen fafatawa.
Lauyan yayi bayanin cewa Keonna ta furta yin biyaya ga kungiyar ta shafin yanar gizo na tweeter, inda take cewa idan suka san zahiri to dukkansu zasu yi rige rigen zuwa su iske yan uwansu a fagagen daga domin su taimaka musu.
Sanarwar ma'aikatar shari'a dake bayanin cajin dake ake yiwa Keonna, tayi zargin cewa Keonna ta nemi samun passpo, kuma tayi ta neman hayoyin zuwa kasar Turkiya ba kai tsaye ba ta internet, harma ta nema kuma ta samu izinin shiga Turkiya ta internet harma ta sayi tikitin tafiya. Ana zargin wannan mace da laifin tuntubar mayakan Islamic state a kasar Syria ta yanar gizo.
Haka kuma an bada rahoton cewa Keonna ta fada wa wata kawarta cewa ta soke shafin ta na tweeter, har sai ta tafi kasar Syria, tana mai fadin cewa bata son ta jawo hankalin wadanda basu yi imanin da abubuwan da yan kungiyar ISIS suke yi ba.
Idan har aka same ta da laifi, ana iya yanke mata hukuncin daurin shekaru goma sha biyar a gidan fursuna.
Mai'aikatar shari'ar Amirka ta bada wannan sanarwa ce, bayan da aka kama wasu mata guda biyu mazauna birnin New York, bisa zargin cewa suna kokarin kera bama a gida da nufin kaddamar da harin ta'adanci cikin Amirka.

XS
SM
MD
LG